Friday, 12 July 2019

Kwantenoni Guda Biyu Makare Da Kayan Bunkasa Wutar Lantarkin Nijeriya Da Aka Yi Odar Su Sun Yi Batar Dabo A Tashar Jirgin Ruwa

Cibiyar kula da wutar lantarkin Nijeriya ta sanar da labarin aukuwar wani al'amari mai kama da al'amara, wato bacewar wasu kayayyakin wutar lantarki da gwamnatin tarayya ta bada odar su domin bunkasa wutar lantarki a fadin kasar nan.


Abin daure kan shine yadda aka rawaito cewa biyu daga cikin kwantenoni uku dake makare da kayayyakin sun yi batar dabo a tashar jirgin ruwa. Sannan shi ma dayan kwantenan da ya rage an gano babu komai a cikinsa, inda ake zargin an wawushe kayan cikinsa.

Sai dai Babban Daraktan na TCN, Usman Gur Mohammed wanda ya sanar da hakan a Abuja a ranar Larabar da ta gabata, bai bayyana ko a wace tashar jirgin ruwan kwantenonin suka bata ba.


No comments:

Post a Comment