Thursday, 11 July 2019

Labarin wasanni: Ban ji dadin canja Ahmed Musa da Koc din Najeriya yayi ba>>Okocha

Labarin wasanni na yau na cewa tsohon tauraron dan kwallon Najeriya, Jay Jay Okocha ya bayyana rashin jin dadinshi da canja Ahmad Musa da kocin Najeriya yayi yayin da ake mintuna 81 da wasa ya sako Moses Simon.Labarain wasannin ya ci gaba da cewa Okocha ya bayyana hakane bayan an tashi wasan da Najeriya ta ci kasar Afrika ta kudu 2-1.

Yace Ahmed Musa ya zamarwa kasar Afrika ta kudu matsala a wasan saboda gudunshi, duk ya rikitasu, kwatsam sai koc ya fitar dashi ya sako Moses Simon, gaskiya ban ji dadin wannan canji ba saboda muhimmancin Ahmed Musa a wasan.

Amma mu bamu isa mu ja da hukuncin Alkalin wasa ba, abin farin ciki shine Moses din ya bayar da taimako an ci kwallo.

Dan haka kamata yayi idan mun yi nasara mu rika yin murna kawai ba dora laifi akan wani dan wasa ba.

No comments:

Post a Comment