Monday, 15 July 2019

Labarin Wasanni: Barcelona ta gabatar da Griezmann tare da bashi lambar da zai goya


Labarin wasanni sun bayyana cewa, Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona a karshe ta gabatar da tauraron dan wasan da ta siyo daga kungiyar Atletico Madrid, Antoine Griezmann. Barca ta siyo Griezmann akan miliyan 120 a cinikin da yake cike da danbarwa.

Madrid ta bayyana lamba 17 a matsayin lambar da zata baiwa sabon dan wasan nata me shekaru 28.

Griezmann ya bayyana cikin rigar Barcelona yana fara'a ya kuma bayyana manema labarai cewa, ina farin ciki da kasancewata anan, na karbi babban kalubale. A shirye nike da duk wani abu da zan fuskanta nan gaba,injishi.
No comments:

Post a Comment