Friday, 12 July 2019

Labarin Wasanni: 'Griezmann ya zama dan wasan Barcelona'

Labarin wasanni da dumi-duminsu daga kasar Sifaniya na cewa Barcelona ta riga ta fitar da kudin sayan tauraron dan kwallon Atletico Madrid, Antoine Griezmann da suka kai Yuro miliyan 120 dan biya.Labaran wasanni na Sport English sun ce tuninan fitar da kudin abinda ake jira kawai shine Barcelona ta sanar da sayen dan wasan a hukumance.

Labaran wasanni daga Marca kuwa na cewa, Griezmann ya riga ya zama dan wasan na Barcelona ma bayan dambarwar da aka sha akan sayen dan wasa wanda tun a shekarar 2017 Barcelonar ta so sayenshi dan ya maye mata gurbin Neymar amma yaki zuwa inda suka kare da sayen Ousmane Dembele.

Hakanan Marca tace Barcelona ta bayyana cewa ba bashin kudin ta ci ba daga asusunta ta fito dasu amma ana sa ran sai zuwa ranar litinin za'a kammala cinikin bayan dan wasan yayi gwajin lafiya a Barca.

Hakanan AS ma ta ruwaito cewa lauyan Griezmann na can ana tattaunawa dashi akan komawar dan wasan Barcelona, kamar yanda labarin wasanninta suka bayyana.

Lokaci dai be bar komai ba.

No comments:

Post a Comment