Thursday, 11 July 2019

Labarin Wasanni: Kalli yanda 'yan kasar Dr Congo sukawa ministan wasannin su dukan kawo wuka saboda fitar dasu daga gasar cin kofin nahiyar Afrika

Wani faifan bidiyo ya bayyana a shafukan sada zumunta wanda rahotanni suka nuna cewa ministan wasannin kasar Dr Congone, Huges Ngouelendele yake shan dukan kawo wuka a hannun 'yan kasar bayan da ya koma kasar bayan da aka fitar dasu daga gasar cin kofin Nahiyar Afrika daga matakin kasashe 16, kamar yanda labarin wasanni na yanzu ya nuna.Kasar madagascar ce ta fitar da Dr Congo daga gasar.

Labarin wasannin na ci gaba da cewa,an ga ministan na kokarin tsira da ranshi bayan da yaga alamun mutanen na kokarin kasheshi.

Hoton bidiyon ya dauki hankula sosai inda da dama ke bayyana ra'ayoyi akai dake cewa indai wannan abu ya tabbata to kuwa lallai babu doka kasar kenan.

Sannan kuma nan gaba watakila idan aka fitar da kasar daga wata gasa, 'yan wasa da koci da minista sai su bari sai 'yan kasar sun huce kamin su koma dan kada a lahantasu.

No comments:

Post a Comment