Tuesday, 9 July 2019

Labarin Wasanni: Real Madrid zata sayar da babban dan wasanta dan samun kudin siyo Pogba

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta bayyana karfin gwiwarta na cewa dan wasan kungiyar Manchester United, Paul Pogba gurinta zai dawo ba tsohuwar kungiyarshi ta Juventus ba, kamar yanda Labarin wasanni ya bayyana.A baya dai wani labarin wasannin na daban ya bayyana cewa, Juventus ma wadda tsohuwar kungiyar da Pogba yawa wasace ta tayashi inda take so ya dawo ya buga mata wasa, hakanan wani labarin wasannin ya kuma bayyana cewa, Cristiano Ronaldo dake Juventus din yana jawo Ra'ayin Pogba zuwa Juventus din maimakon Real Madrid.

Manchester United dai ta sakawa Pogba farashin fan miliyan 150 ga duk kungiyar dake son sayenshi, kamar yanda labarin wasannin da Mail ta ruwaito suka bayyana.

Hakanan a yanzu, ita Real Madrid bata da wadannan kudin a kasa, ko kuma ana iya cewa, watakila idan ta fitar dasu ta sayi pogban akai tsaye, zata takura. Zabin da ya rage mata a yanzu shine ta sayar da dan wasa dan samun cikon kudin da sata siyo Pogban cikin tsanaki.

Saidai duk kokarin Real Madrid na sayar da babban dan wasanta, Gareth Bale ya faskara, kamar yanda Labarin wasanni ya bayyana a baya, dan haka yanzu ta daga dan wasanta, James Rodriguez zata sayarwa da kungiyar Napoli shi akan miliyan 40.

Saidai ana neman samun cikas a wannan ciniki tsakanin Napoli da Real Madrid saboda ita Napoli tana son a bata damar biyan kudin dan wasan da kadan-kadan amma ita Real Madrid kuwa so take a bata kudi hannu dan samun sayen Pogba kamin karshen watannan na Yuli da muke ciki, kamar yanda labarin wasannin ya bayyana.

No comments:

Post a Comment