Wednesday, 10 July 2019

Labarin Wasanni: Yanda Senegal ta kai ga wasan kusa dana karshe bayan cin Benin 1-0

Labarin wasanni na yammacin yaudai ba zai kammalu ba idan ba a saka yanda kasar Senegal ta lallasa kasar Benin da ci daya me ban haushi ba a ci gaba da gasar neman daukar kofin nahiyar Afrika ba.An yi gumurzu inda har aka tafi hutun rabin lokaci babu wanda ya ci kwallo tsakanin kasahen, bayan dawowa daga hutun rabin lokacine sai Idrissa Gana Gueye na kasar Senegal ya ci mata kwallo ana mintin 70 da wasa kuma a haka aka tashi wasan.

Kasar ta Senegal itace ta farko da ta fara kaiwa ga wasan kusa dana karshe a gasar sannan kuma labarin wasanni na hutudole.com ya samu na cewa wannan ne karin farko cikin shekaru 13 da kasar ke kaiwa ga wannan matsayi a gasar, rabonta da haka tun shekarar 2006.

No comments:

Post a Comment