Friday, 12 July 2019

Labarin Wasanni: An yanka ta tashi: Atletico Madrid ta ce bata yadda da cinikin Griezmann ba an cuceta dan haka zata je kotu

Bayan sanar da sayen Antoine Griezmann da kungiyar Barcelona ta yi daga Atletico Madrid akan Yuro miliyan 120 a yau, Atletico Madrid ta bayyana cewa bata yadda da wannan ciniki ba kuma zata garzaya kotu.Labarin wasanni ya ci gaba da cewa, a sanarwat data fitar bayan cinikin, Atletico Madrid ta bayyana cewa asalin kudin da ta sawa Griezmann idan wata kungiya na son sayenshi Yuro miliyan 200 ne amma daga baya sai ta rageshi zuwa Yuro miliyan 120.

Saidai Atletico Madrid tace Barcelona da Griezmann sun kammala ciniki tsakaninsu tun kamin ta ragewa dan wasan kudi, lura da irin alamun da dan wasan ya rika nunawa, kuma sun kammala wannan ciniki ne tun karshen kakar wasan data gabata.

Dan haka Atletico Madrid tace ba ta yadda da wannan ciniki ba, ko dai Barcelona ta ciko mata Yuro miliyan 70 ko kuma ta garzaya kotu.

No comments:

Post a Comment