Friday, 12 July 2019

Labarin Wasanni:AFCON:Tunisia zata hadu da kasar Senegal a wasan kusa dana karshe

Kasar Tunisia ta fitar da kasar Madagascar daga gasar cin kofin nahiyar Afrika a wasan da suka buga jiya inda ta saka mata kwallaye 3-0. Wannan na nufin kasar Tunisia ta kai wasan kisa dana karshe inda zata hadu da kasar Senegal.Za'a buga wasannin na kusa dana karshe ne tsakanin kasashen biyu ranar Lahadi me zuwa da misalin karfe 5 na yamma idan Allah ya kaimu, kamar yanda labarin wasanni suka bayyana.

No comments:

Post a Comment