Saturday, 13 July 2019

Lukaku zai ci gaba da 'zama' a Manchester United

Da alamu Romelu Lukaku zai ci gaba da zama Manchester United duk da cewa Inter Milan ta nuna sha'awar sayanshi.


An yi hasashen Inter za su dauki dan wasan mai shekara 26, bayan da aka nada mutumin da ya dade yana sha'awar Lukaku, Antonio Conte a matsayin kocin Inter.

Sai dai kawo yanzu babu tayi da aka gabatarwa United. Kuma ko da an gabatar, United za ta so farashin ya haura fam miliyan 75 din da ta biya Everton shekara biyu da ta gabata.


Lukaku ya zura kwallo 42 a wasa 96 da ya buga tun komawarsa United.

Majiyoyi da dama sun tabbatar da cewa Manchester United ba ta sanya farashi kan dan kwallon ba, wanda har yanzu yana da sauran shekara uku a kwantiraginsa.

Haka kuma ana ganin dokar kashe kudade ta hukumar kwallon Uefa ta sa dole sai Inter ta sayar da 'yan wasa kafin ta iya sayen Lukaku.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment