Saturday, 13 July 2019

Magoya bayan Atletico Madrid sun lalata Tambarin sunan Griezmann: Dan wasan ya mayar da martani kan kalaman kungiyar


La placa de Griezmann fue atacada.
Masoyan kungiyar Atletico Madrid sun lalata tambarin sunan Antoine Griezmann da aka buga a jikin filin wasan kungiyar dan karramashi a matsayin wanda ya bugawa kungiyar wasanni 100. Masoyan kungiyar sun lillika wasu fastoci da kuma watsa kasa a jikin sunan Griezmann din bayan komawarshi Barcelona.

Barcelona ta biya Yuro miliyan 120 akan Griezmann duk dacewa dai Atletico Madrid din ta nuna kin amincewa da farashin sannan ta yi barazanar garzayawa ga FIFA dan kai kara.

Ba wannan ne karin farko da magoya bayan kungiyar ke ciwa tambarin sunayen 'yan wasa mutunci ba bayan sun bar kungiyar, sun yiwa 'yan wasa irin su Thibaut CourtoisHugo Sánchez da Sergio Agüero wannan abu.
Griezmann lawyer: "Atlético has acted in bad faith"

A wani labarin Wasanni na Griezmann da muka samu shine lauyan dan wasan, Sevan Karian ya mayarwa da Atletico Madrid da martani akan cewa da ta yi Turo miliyan 200 ya kamata Barcelona ta biyata ba Yuro miliyan 120 ba saboda dan wasan da Barca tun kamin a rage mai kudi suka yi ciniki akan komawarshi kungiyar, shugaban Atletico Madrid, Enrique Cerezo ya bayyana cewa suna da hujja akan hakan.

Saidai lauyan na Griezmann ya bayyana cewa dan wasan baiji dadin wadannan kalamai da suka fito daga tsohuwar kungiyar tashi ba dan ba abinda suka gayamai kenan ba a asirce.

Lauyan ya gayawa jaridar faransa,  L’Equipe cewa zasu dauki matakin daya dace akan barazanar da Atletico ta yi na kai karar Barcelona akan cinikin

No comments:

Post a Comment