Thursday, 11 July 2019

Majalisar wakilai ta nemi Buhari ya saki Sheikh Zakzaky

Majalisar wakilan Najeriya ta yi kira ga gwamnatin kasar da ta saki jagoran kungiyar 'Yan Uwa Musulmi ta 'yan Shi'a kamar yadda wasu kotunan kasar suka bayar da belinsa a baya.


Majalisar ta amince da wannan kuduri ne kwana guda bayan taho-mu-gamar da aka yi tsakanin 'yan sanda da kuma mabiya Sheikh Ibrahim Elzakazaky a harabar majalisar, lamarin da ya haifar da asarar rayuka, sannan ya kai ga dage zaman majalisar.

Honourable Abdurrazak Namdas, mai magana da yawun majalisar na riko, ya shaida wa BBC cewa a matsayinsu na wakilan jama'a suna ganin ya dace a saki jagoran na 'yan Shi'a domin wanzar da zaman lafiya.

Tun shekarar 2015 ne ake tsare da Sheikh Zakzaky bayan wani hari da jami'an tsaro suka kai wa magoya bayansa a Zariya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum fiye da 300.

Tun lokacin ne kuma mabiyansa ke ta zanga-zangar neman a sako shi, suna masu zargin cewa "yana cikin mummunan yanayin rashin lafiya".


Dan majalisa Namdas, ya ce wannan ne ya sa 'yan majalisa suka nuna cewa tun da har sun dade suna zuwa suna nuna rashin jin dadinsu, to ya kamata mu saurare su.

"Ya kamata a saurari 'yan Shi'a domin ba mu san abin da ke zukatansu ba."

"Tun da kotu ta ba shugabansu beli, ya kamata mu saurare su domin rashin saurarensu na iya haifar da matsala, kamar rikicin Boko Haram."

"Kan haka ne majalisa ta ga ba laifi ba ne a bada belin Zakzaky," in ji shi.

Sai dai babu tabbas ko Shugaba Muhammadu Buhari zai ji wannan kira na majalisar, kuma Namdas ya ce shawara ce kawai suke bayarwa domin ganin an samu zaman lafiya.

Bayan tarzomar da ta barke a ranar Talata, rundunar 'yan sandan Najeriya ta sanar da daukar tsaurara matakan tsaro a ciki da wajen babban birnin kasar Abuja, tare da gargadin masu tada zaune tsaye su guji fushin hukuma.

Jami'an tsaro sun zargi 'yan Shi'a da harbar musu mutum biyu tare da jikkata wasu shida, sannan suka ce sun kama mambobin kungiyar guda 40.

To sai dai Muhammad Ibrahim Gamawa daya daga cikin masu magana da yawun 'yan Shi'ar ya musanta zarge-zargen 'yan sandan, inda ya ce ba su da makaman da 'yan sandan suka ce sun yi harbi da su.

Ya kuma kara da cewa sabanin mutum 40 da rundunar 'yan sandan ta ce ta kama musu, an "kama mana kusan mutum 100."
BBChausa.

No comments:

Post a Comment