Monday, 1 July 2019

Manyan 'yan wasan Barcelona 4 da zasu bar kungiyar a yau

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona zata rabu da 'yan wasanta 4 a yau Litinin kamar yanda tahotanni suka bayyana, tuni dai Barca ta sayar da jesper Cillessen ga Valencia sai kuma Andre Gomes da ya koma Everton.'Yan kwallo 4 da zasu bar Barcelona yau, Litinin sune, Thomas Vermaelen, Jeison Murillo, Kevin-Prince Boateng da Douglas Pereira, kamar yanda Mirror ta ruwaito.

A yau, Litinin kwantirakin Thomas Vermaelen, wanda tsohon dan wasan Arsenal ne ke karewa a Barcelona kuma basu bashi damar sake ci gaba da zama a kungiyar ba, wannan yasa dole ya tafi a matsayin kyauta ga wata kungiyar.

Su kuwa Murillo da Boateng dama sun zo Barcelonane a matsayin aro kuma a yau zaman nasu ke karewa a kungiyar dan haka zasu koma kungiyoyinsu na asali.

Pereira kuwa wanda dama yana aro a wata kungiyar shima Barcelona bata bashi damar ci gaba da zama a kungiyar ba dan haka shima zai koma wata kungiyar a kyauta.

No comments:

Post a Comment