Thursday, 4 July 2019

Maryam Yahaya ga mijin aure

Ga dukkan alamu Burin Tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Yahaya na samun mijin aure ya cika. A 'yan kwanakinnan ne rahotanni suka watsu cewa jarumar ta bayyana cewa tana son aure a wata hira da ta yi da gidan Freedom Radiyo.Cikin hanzari, sanannen masoyinnan nata dan sandan, Rilwanu bala ya mayar da martani inda ya rubuta a shafinshi na Facebook cewa a shirye yake ya aureta.

Ga sakonshi kamar haka:

Jiya farin ciki bai barni na yi bacci ba saboda yadda na ji gidan redio Freedom ya yi hira da jaruma Maryam Yahaya kuma ta ce idan ta samu miji za ta yi aure. 

Hakika zuciyata tana matukar kaunar Maryam yahaya, kuma a shirye nake na
aure ta matukar za ta amince. 

Ba na jin tsoron duk wanda zai fito ya ce yana son ta a fadin Nigeria. Amma ina matukar jin tsoron ta ce ba za ta amince da ni ba, kamar yanda ya aikawa Sarauniya.

No comments:

Post a Comment