Friday, 19 July 2019

Masoya sun fado daga bene hawa 9 yayin da suke jima'i

Wasu masoya biyu sun fado daga bene hawa 9 a yayin da suke jima'ai kuma macen ta mutu amma namijin da ya fado kanta ya sha. Lamarin ya faru ne a St Petersburg, kasar Rasha.Rahotanni sun bayyana cewa masoyan da macen shekarunta 30 shi kuma namijin shekarunshi 29 suna shan wani casune a gidan nasu.

Sai suka zo kan tagar dakin nasu suna abin, nane sai talabijin ta fado kasa, bayannan kuma sai macen ta fado ta kai, inda nan take ta mutu, shi kuma namijin ya fado amma ba kai tsaye kasa ba, inda bishiyoyi suka tareshi sannan ya fado kan matar.

Fadowarshi ke da wuya ya tashi ya kakkabe jikinshi ya koma sama da gudu.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa, namijin gajeren wando ne kawai a jikinshi, yayin da shi kuma mace daga kugunta zuwa kasa bata saye da komai.


No comments:

Post a Comment