Thursday, 11 July 2019

Muma a shirye muke mu raba gari da Neymar>>PSG

Kungiyar kwallon kafa ta PSG ta ce a shirye ta ke ta raba gari da Neymar matuka ta samu tayi mai gwabi da zai mayar mata da kudaden da ta bannatar akan dan wasan ko da kuwa daga wane Club ne.A cewar Leonardo Araujo manajan wasanni na PSG, kawo yanzu babu Club din da ya nuna bukatar sayen dan wasan hatta Barcelonar da ya ke fatan komawa.

Neymar dan Brazil mai shekaru 27 wanda ya koma PSG daga Barcelona kan yuro miliyan 222 a shekarar 2017, har yanzu ya na da sauran wa’adin shekaru 3 kafin karewar kwantiraginsa, sai dai ya ce ya na son sauya sheka ne saboda matsalar da yak e fuskanta da yanayi a Faransa.

Ko a kakar wasa da ta gabata an ga yadda Neymar ya bata kusan watanni 5 ya na jinyar rauni.

A cewar Leonardo, Club din na PSG kan sa baya bukatar ‘yan wasan da za su rika jin sun yiwa Club din alfarma saboda kasancewarsu a cikinsa, sai dai wadanda za su yi alfahari da kasancewar su ‘yan wasansa.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment