Wednesday, 10 July 2019

Mutum biyar da arzikinsu ya fi kasafin kudin Najeriya

Wani rahoton da kungiyar agaji ta Oxform ta fitar ya bayyana irin mummunar tazarar da ke tsakanin masu kudi da talakawa a yankin Afirka ta Yamma.


Rahoton ya ce masu kudin yankin guda 10 sun fi kasashe 16 na yankin arziki.

Oxform ta ce kasashen Afirka ta Yammar na asarar akalla dala biliyan 9.6 a kowacce shekara ta hanyar dage haraji ga kamfanonin kasashen duniya.


Irin wadannan kudaden, in ji rahoton, za a iya amfani da su wajen gina asibitocin zamani guda 100 a kowace shekara a yankin.

Najeriya ce ta fi kowacce kasa arzikin man fetur a Afirka, amma 'yan kasar da dama na fama da zazzafan talauci, wanda ake alakantawa da cin hanci da rashawa da kuma rashin adalcin shugabanni.

Masu arzikin Najeriya
Rahoton Oxform ya ce mutum biyar masu arzikin Najeriya da arzikin nasu ya kai dala biliyan 29.9, ya yi wa kasafin kudin kasar na shekarar 2017 shal wanda ya kama naira tiriliyan 7.29, kwatankwacin dala biliyan 23.97.

Jaridar Forbes ta wallafa sunayen mutum biyar 'yan Najeriyar da suka fi arziki a kasar kamar haka:

Aliko Dangote
Mike Adenuga
Abdul Samad Rabiu
Folorunsho Alakija
Femi Otedola

To sai dai Oxform ta kara da cewa kusan kaso 60 cikin 100 na 'yan kasar na rayuwa ne a kasa da dala 1.9 a kullum, wata alama ta girman kangin talauci a kasar.

Kuma mata su ne kaso 60 zuwa 79 na masu aiki a karkara a Najeriya, amma kuma ba sa iya mallakar kasar noma.

Ghana
A Ghana, wadda ita ce kasa ta biyu mai karfin tattalin arziki a yankin Afirka ta Yamma, rahoton ya ce a wata daya mutum daya daga cikin mafiya arziki a kasar na samun abin da mata matalauta za su samu a shekara 1,000.

Oxform ta kara da cewa a 2016, kasar ta Ghana ta samu karin mutane 1,000 da suka zama miloniyoyi, inda kuma aka samu fiye da karin matalauta miliyan daya.

Rahoton ya ci gaba da yin tsokaci kan Afirka ta Yamma, yana mai cewa yankin ya samu habakar tattalin arziki a shekaru 20 da suka gabata.

A 2018, yankin ya samu kasashe shida da tattalin arzikinsu ya habaka.

Kasashen sun hada da Kwaddibuwa da Senegal da Ghana da Burkina Faso da Benin da kuma jamhuriyar Nijar.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment