Sunday, 21 July 2019

Mutumin da yafi Hitler ta'addanci

Idan ana maganar kisan kare dangi a wannan zamanin da muke ciki, mafi yawawanci wanda ake kira shine Adolf Hitler saboda kisan da yawa Yahudawa saidai akwai wanda yafishi. King Leopold II sarkin kasar Belgium ne da aka haifa a 1935, shekaru 184 da suka gabata.A kiyasi Hitler ya kashe yahudawa miliyan 6 kuma da dama sun yi ittifakin cewa dalilin da yasa aka fi yayatashi fiye da King Leopold shine saboda shi Hitler turawa ya kashe yayin da shi kuwa Leopold Bakar fata ya kashe.

Bakar fatar da Leopold ya kashe an yi kiyasin cewa sun ninka mutanen da Hitler ya kashe fiye da sau biyu inda ake maganar mutane miliyan 15. Amma wasu gwanayen tarihi na tantama akan yawan mutanen da Leopold ya kashe tunda sunce babu wata madogara me karfi dake tabbatar da hakan.

Amma dai duk da haka Leopold yayi abinda su kansu turawan mulkin mallaka sun kadu da lamarinshi sosai.

A yayin da kasashen turai suka fara yiwa sauran kasashen Duniya mulkin mallaka, sai abin ya koma gasa tsakaninsu, saboda ana ganin cewa akarfi da shaharar kasa ya ta'allakane ga yawan kasashen da takewa mulkin mallaka Da kuma yawan arzikin da take tatsa daga wadannan kasashe.

Wannan yasa King Leopold shima yace ba za'a bar kasarshi ta Belgium a baya ba. Dan haka bayan da ya zama sarki a shekarar 1865 sai shima ya fara nemawa kasarshi yankin da zata wa mulkin mallaka.

Ya nemi yiwa kasar Philippines da a wancan lokacin ke karkashin ikon sarauniyar Sfaniya Queen Isabella mulkin mallaka inda ya nemi ta bashi iko da kasar, saidai wannan kudiri nashi be cika ba saboda kamin kammala tattaunawar sai akawa sarauniyar juyin mulki.

Da yaga wannan damar ta kubuce mai, sai ya juyo zuwa yankin Afrika inda ya kafa wata kungiya da yawa lakabi ta bincike da kawo ci gaba a yankin Afrika ta hanyar yada addinin kiristanci, kawo kayan sawa da sauran abubuwan ci gaba yankin.

King Leopold ya samu rancen kudi daga gwamnatin kasarshi ta Belgium dan gudanar da wannan aiki, inda da yawa sukawa kallon aikin sa kai na neman lada ne wanda babu son kai a ciki.

A taron Berlin Conference na shekarar 1885 da kasashen yamma suka kasaftawa kansu nahiyar Afrika dan yi mata mulkin mallaka, King Leopold ya samu amincewar kwamitin kasashen turawa ya mulki yankin Congo da ya sakawa sunan Congo Free State.

Bayan da Leopold ya kammala biyan gwamnatin kasarshi bashin data bashi sai kasar Congo ta koma mallakinshi shi kadai duk arzikin kasar gurinshi yake zuwa, maimakon kasa kamar yanda sauran kasashe ke mulkin mallaka, saidai aniyarshi ta yada addinin kiristanci da samar da kayan sawa gaba daya ta canja inda ya koma neman azurta kanshi ido rufe. Kasashen dake mulkin mallaka a bisa al'ada sukan fito da hanyoyin zalunci da mummunan horo dan su samu abinda suke so amma irin abinda King Leopold yayi ya matukar tsoratar da sauran kasashen turawa.

Da farko dai ya haramtawa duk wata kasa shiga kasar ta Congo sannan kuma ya hada kai da wani balarabe me cinikin bayi, Tippu Tip wanda shi dama Ya dade yana zaune a yankin Congo, duk da cewa ana kokarin hana bauta a lokacin sai King Leopold ya hada baki da Tip akan cewa zai bashi gwamnan yankin da yake da zama amma kada ya saka mai ido akan abinda zai yi.

Tippu ya yadda da wannan sharadi inda shi ya ci gaba da cinikin bayinshi abinshi. Saidai bayan da labari ya kaiwa sauran kasashen Turawan dake mulkin mallaka, sun nunawa King Leopold rashin yadda da hada kai da Tippu da yayi inda suka ce mai dole ya warware yarjejeniyar dake tsakaninsu.

Maimakon ya bi ta hanyar lalama, King Leopold ya hada rundunar yaki ta musamman wadda ta yaki Tippu da sauran larabawan dake Congo inda aka kashe mutanen da ba'asan adadinsu ba. Bayan nasara akan Tippu sai King Leopold ya nada gwamnoninshi inda ya basu aikin samo gwal, Roba, hauren giwa, dadai sauran ma'adanai.

Ana biyan kowane gwamna Albashine bisa la'akari da yawan arzikin da ya kawo daga yankinshi, dan haka kowane daga cikinsu ya dukufa dan ganin an samo arziki me yawa.

Masu bayar da tarihi da dama kan kira King Leopold da sunan shedan da ya mayar da Conga kamar wata kwarya-kwaryar wutar jahannama, sannan yana da gwamnoni marasa Imani da akewa lakabi da Shedan, me cire kai da me gasawa 'yan Congo aya a hannu. kowane mutum a Congo an bashi yawan arzikin da ake so ya hako ko ya kawo, idan mutum bai kawo yawan da aka bukaceshi ya kawo ba, to za'a yanke mai kafa daya ko hannu, idan kuma yana da kwazo wajan aiki to sai a yankewa matarshi ko danshi kafa daya ko hannu.

Hakanan idan ya sake gazawa za'a sake yanke dayar kafar ko hannun, King Leopold nada dakunan tara gundulmin hannu dana kafafu dan nunawa mutane dan su tsorata dashi sannan kuma yana da dakunan da aka ware dan yiwa matan bakaken fata fyade.
Wannan wani mutum ne ke kallon kafa da hannun diyarshi 'yar shekaru 5 da aka guntule saboda bai kai yawan ma'adanan da aka bukaceshi kaiwa ba

An rika amfani da salon da aka yi amfani dashi a yakin Duniya na 1 watau kashe wanda aka ga baida sauri wajan aiki, ko kuma asa mutum yayi ta aiki ba hutawa har sai ya mutu, sannan gwamnonin King Leopold sun rika tirsasawa bakar fata shiga ramin hakar ma'adanai suna mutuwa a yayin aiki, ba'a san yawan wanda suka mutu ta irin wannan hanyaba.

A karshe dai labarin mulkin King Leopold a Congo ya kai kunnen sauran kasashen yamma dake gasa dashi wajan tara Dukiya, dan haka sai aka yi caaa akanshi sannan aka tursasashi ya mayar da mulkin Congo zuwa gwamnatin kasar Belgium a shekarar 1908, saidai shekaru 6 kaminnan wani dan kasar Italiya, Gennaro Rubino yayi yunkurin kashe King Leopold har sau 3 amma bai yi nasara ba.

Saidai dan kada a gane irin kazamin mulkin da yayi a Congo, King Leopold ya kone duk wata takardar tarihin aikin da yayi dana kasar Congo kurmus, wanda sai da suka kwana 8 suna ci da wuta.

A karshe har bugun kirji yayi inda Ya fadi cewa "Zasu iya kwace Congo daga gareni amma basu isa su san irin mulkin da nayi ba"

King Leopold ya mutu a shekarar 1909.

Bayan komawar kasar Congo karkashin mulkin kasar Belgiun an canja maya suna daga Congo Free state zuwa Belgian Congo, sannan an yi tsare-tsare na ganin cewa an daina kashe mutane haka siddan da kuma canja tsarin biyan gwamnoni bisa la'akari da yawan arzikin da suka tara zuwa sai an gamsu da aikin gwamna ko kuma ya kammala aikinshi sannan za'a biyashi.

Saidai rahotanni sun bayyana cewa har bayan da gwamnatin kasar Belgium ta karbi mulkin Congo an ci gana da yankewa mutane hannu da kafafu da kuma yi musu bulala har zuwa lokacin da kasar ta samu 'yancin kai a shekarar 1971.

Kuma rahotanni sun bayyana cewa har yanzu akwai yankunan kasar Congo dake da Albarkatun kasa wanda turawa ne ke rike da iko dasu, sun samu lasisin mallakar gurarenne daga majalisar dinkin Duniya.

Bayan mulkin Leopold a Congo an yi kidaya inda aka samu mutane miliyan 10 a kasar. Babu wanda yasan yawan mutanen dake kasar ta Congo kamin mulkin Leopold dan hakane ma wasu ke tantamar yawan mutanen da akace Leopold ya kashe basu kai miliyan 15 ba amma da dama wanda suka rubuta tarihin mulkin firaunancin Leopold a Congo sun ce sai da ya kashe rabin al'ummar kasar, kuma sun sami wadannan alkalumane ta hanyar ji ta bakin mutanen kasar da kuma sauran burbushin tarihin da ya rage.


No comments:

Post a Comment