Saturday, 13 July 2019

Najeriya na samun Nasara a yaki da ta'addanci>>Shugaba Buharu

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari kenan a wadannan hotunan tare da gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai da kakakin majalisar dattijai, Ahmad Lawal da sauran mukarraban gwamnati a wajan yaye mayan hafsoshin soji da aka yi a Kaduna.

Da yake jawabi a gurin taron shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa matsalolin tsaron dan Najeriya ke fuskanta yawanci na samuwane daga kan iyakokin kasarnan shiyasa Najeriya da kasashen Afrika ke bukatar hadin kai dan yin harkar tsaro tare.

Najeriya ta yi hadaka da kasashen Nijar, Kamaru da Chadi wajan yakar Boko Haram kuma kwalliya na biyan kudin sabulu injishi dan yanzu anci karfin 'yan ta'adda injishi.

Shugaban yace a yakin da Najeriya ke yi da ta'addanci bisa hadin gwiwar kasashe makwabta ba zata yi kasa a gwiwa ba sai ta ga karshen lamarin.

Shugaban ya kuma yabawa sojojin inda yace suna kokari wajan yaki da Boko Haram da masu garkuwa da mutane da kuma masu neman ballewa.
No comments:

Post a Comment