Wednesday, 10 July 2019

Nicki Minaj ta fasa zuwa Saudiyya

Shahararriyar mawakiyar nan 'yar Amurka, Nicki Minaj, ta fasa yin wasan da za ta yi a makon gobe a kasar Saudiyya.


A makon jiya ne aka bayyana mawakiyar a matsayin wadda za ta yi wasa a dandalin wani taron raye-raye na shekara-shekara a birnin Jeddah, abin da ya jawo suka a ciki da wajen kasar.

Ta ce goyon bayan da take nuna wa mata da kungiyoyin kare 'yancin 'yan luwadi da madigo a matsayin dalilan da za su hana zuwa kasar.


Yayin da wasu suke adawa da ziyarar da za ta kai kasar saboda yadda kasar ta yi kaurin suna wajen take hakkin dan Adam.

An shirya mawakiyar hip pop din ta Amurka za ta gabatar da wasan ne a bikin Jeddah World Festival ranar 18 ga watan Yuli da muke ciki.

Wasan da za ta yi yana daya daga cikin irin sauye-sauyen da Saudiyya ke samarwa game da harkar nishadantsarwa a kokarinta na habaka bangaren adabi a kasar.

Sunan "Nicki Minaj" yana cikin kalmomin da suka yi fice a shafin Twitter a ranar Larabar da ta gabata yayin da mutane ke ta bayyana ra'ayoyinsu game da ziyarar.

Wani mai amfani da shafin ya ce: "A ce kawai yanzu kana farkawa daga dogon suma a fada ma cewa Nicki Minaj za ta yi wasa a Saudiyya, ai zan zaci cewa a wata duniyar daban na farka."

Shi kuwa wannan tambaya yake kan ko an nemi karin bayani a kan Nicki Minaj a Google kafin a gayyato ta:

Ra'ayoyin ba duka ne masu sauki ba da kuma goyon bayan abin. Wani ya ce sam abin bai dace ba in aka kalli kusancin garin Jeddah da Makkah gari mafi tsarki a duniya.

Ita kuwa wata mata bidiyo ta wallafa a shafinta, inda take korafin cewa ta yaya za a gayyato Nicki Minaj Saudiyya kuma a tilasta masu saka doguwar abaya.

"Za ta zo ta yi murgude-murgude kuma ta yi wakoki kan jima'i da fitsara amma kuma ku ce min na saka abaya. Shirme kenan?"

Wasu kuwa sun bayyana cewa zuwanta kasar yunkuri ne kawai na yada madigo ganin yadda kasar take da tsauri kan 'yan luwadi da madigo - hukuncin kisa ne ake yanke wa 'yan luwadi da madigo a Saudiyya.

Minaj ba ita ce ta farko ba da ta haddasa ce-ce-ku-ce a kan amsa gayyatar yin wasa a kasar.

Mawakiya Mariah Carey ma ta gabatar da nata wasan duk da irin kiraye-kirayen da masu fafutikar kare hakki suka yi mata da kada ta yi.

Mawaki Nelly ma ya sha suka sosai bayan ya gabatar da wasan maza zalla a kasar.

Wannan sassauci kan harkokin nishadantarwa na baya-bayan nan da Saudiyya ke yi wani bangare ne na shirin da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman yake yi na fadada harkokin tattalin arzikin kasar.

Turki Al al-Sheikh shi ne shugaban hukumar nishsadantarwa ta kasar kuma tun a watan Janairu ya shimfida hanyar ciyar da bangaren gaba a wani sako da ya wallafa a Twitter.

"Da yardar Allah alkiblar harkar nishadi a shekaru masu zuwa za ta kasance ta hanyar hada tarukan wasanni na dandali da wuraren shakatawa da wasannin kwaikwayo domin ci gaban matasa da kuma tallafa wa kamfunnan nishadantarwa na kasa."
BBChausa.

No comments:

Post a Comment