Monday, 1 July 2019

Real Madrid zata baiwa Liverpool dan wasanta hadi da kudi ta karbi Sadio Mane

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid na shirin baiwa Liverpool dan wasanta, Marco Asensio inda ita kuma take bukatar Liverpool ta bata dan wasanta Sadio Mane.Rahoton Expressuk na cewa, Real Madrid na son hadawa Liverpool da kudi hadi da Asensio dan su amince da wannan ta yi.

Mane ya ci kwallaye 26 jimulla a dukkanin gasar kwallon da ya buga a kakar wasan 2018/19 sannan ya taimakawa Liverpool din ta dauki kofin Champions League, ana ganin wannan daliline yasa idon Madrid ya kai kan dan wasan.

No comments:

Post a Comment