Sunday, 14 July 2019

Ronaldo ya koma Atisaye a Juventus bayan hutu, ya kuma bayyana sabon takalmishi na musamman

Tauraron dan kwallon kafara kasar Portugal me bugawa Juventus wasa, Cristiano Ronaldo kenan a wadannan hotunan yayin da ya halarci kungiyar tashi ranar Asabar dan yin gwajin lafiya da fara Atisaye bayan dawowa daga hutu.Masoyan Ronaldon da damane suka tarbeshi  a filin wasan inda suka mai maraba da zuwa.

Ronaldo ya kuma bayyana sabon takalminshi da zai yi amfani dashi wajan buga wasannin sada zumunci da zasu yi da Inter Milan a kasar China.
Za'a buga wasanne tsakanin kungiyoyin kishiyoyin juna a karshen watannan da muke ciki.


No comments:

Post a Comment