Saturday, 13 July 2019

Ronaldo ya Koma Juventus dan soma Atisaye


Tauraron dan kwallon Juventus, Cristiano Ronaldo ya kammala hutunshi na karshen kakar wasa inda ya zagaya Duniya da iyalanshi, a yanzu ya koma Turin kasar Italiya inda zai fara atisaye karin farko tare da sabon me horas da 'yan wasa, Maurizio Sarri.

Ronaldo ya sauka a filin jirgi jiya inda ya hau motar alfarma ta Rolls Royce da dama take ajiye tana jiranshi.

A yau Sabarne Ronaldon zai koma fagen atisaye a Juventus.

No comments:

Post a Comment