Thursday, 11 July 2019

Saudiyya za ta dauki matakan hana Mahajjata bayyana Mazhaba Ko Akidarsu a lokutan aikin Hajji

Gwamnatin Masarautar Saudiyya ta bayyana cewa za ta dauki matakan hana Mahajjata bayyana Mazhaba ko Akidar siyasarsu a lokutan aikin Hajji.


Kamfanin dillancin labarai na Saudiyya ya fadi cewar an gudanar da taron Majalisar Ministoci a Jidda karkashin Yarima Mai Jiran Gado Muhammad bin Salman.

Bayan taron an fitar da rubutacciyar sanarwa wadda ta yi kira ga Mahajjata da su mayar da hankali kan aikin Hajji kadai inda aka gargade su da su nisanci bayyana Mazhaba ko bangaren siyasar da suke.

Sanarwar bayan taro ta kuma ce, a lokacin Ibadar Hajji ana bukatar nutsuwa da daidaituwa a saboda ahaka ana bukatar Mahajjata da su nisanci duk wata dabi'a da za ta bata wadannan abubuwa, kuma ba za a lamunci duk wani da zai karya wannan doka ba.

An kuma bayyana za a dauki dukkan matakan da za su dakile duk wani yunkuri na wani da zai karya wannan doka.
TRThausa.


No comments:

Post a Comment