Saturday, 13 July 2019

Shaidu sama da 500 zasu bayar da shaida a kotu kan cewa gwamna Gandujene ya lashe zaben gwamanan Kano


Shaidu sama da dari 500 zasu bayyana a gaban kotun sauraren karar zabe dake Kano dan bayar da shedar cewa gwamnan Kanon, Dr. Abdullahi Umar Gamdujene ya lashe zaben da aka gudanar a watan Maris na wannan shekarar.

Lauyan Gandujen, Offiong Offiong (SAN) ya bayyanawa kotu a ranar Asabar cewa yana da shaidu 203 da zasu bayar da sheda a gaban kotun kan cewa gwamnan Gandujene ya lashe zaben kuma duka shaidun sun cika sharuddan da doka ta tanada.

Hakanan lauyan APC, Christopher Osiomole ya bayyana cewa itama jam'iyyar tana da shaidu 300 da zasu bayar da shaida akan cewa dan takararsune ya lashe zaben gwamnan jihar.

Hakanan itama hukumar zabe me zaman kanta, INEC ta bayyana ta hanyar lauyanta, Ahmed Raji(SAN) cewa tana da shaidu 29 da zasu bayar da shaida a gaban kotun akan sahihancin zaben data gudanar a jihar.

Shi kuma lauyan PDP, Adegboyega Awomolo(SAN) ya bayyana cewa, suna da shaidu 203 da zasu bayar da shida akan cewa ba gwamna Gandujene ya lashe zaben jihar ba.

Da take magana akan fara sauraren kasarar, Justice Halima Shamaki ta bayyana cewa ta daga ci gaba da share fagen sauraren karar zuwa 16 ga watan Yuli.

No comments:

Post a Comment