Saturday, 13 July 2019

Shari'ar Buhari da Atiku: An kai wa shaidun Atiku 'hari'

Kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa a Najeriya ta dage zaman shari'ar da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ya shigar na kalubalantar zaben da ya gabata.


Dole ce ta sanya kotun daukar matakin sakamakon harin da aka kai wa shaidu daga bangaren jam'iyyar PDP akan hanyarsu ta zuwa Abuja daga jihar Zamfara.

Rahotanni sun bayyana cewa barayi ne suka afkawa mutanen akan hanyar ta su, inda dole suka bazama dazukan da ke kusa domin tsira da rayukansu.


Hukumar zabe ta INEC ta bayyana Shugaba Muhammadu Buhari na APC a matsayin wanda ya lashe zaben na watan Fabrairu, kuma tuni aka rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu kamar yadda tsarin mulki ya tanada.

Sai dai Atiku Abubakar da jam'iyyarsa ta PDP sun ce su ne suka "lashe zaben amma aka murde musu," a don haka suka garzaya kotun domin neman hakkinsu.

Tun da fari a ranar Juma'a, dan takarar shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar da jam'iyyarsa ta PDP sun gabatar da shaidu guda bakwai, da suka hada da jami'an kananan hukumomi, kamar yadda lauyan wanda ya shigar da kara Chris Uche ya bayyana.

Harwayau, jagoran lauyoyin PDP Levy Uzoukwu ya yi ikirarin shaidun da suka tsere sun tuntube shi ta wayar tarho.

Hakan ne ya sa ya yi kira ga kotun da ta dage zaman shari'ar domin su samu damar sake kiran shaidun su bayyana gabanta.

Alkalin da ke jagorantar shari'ar Muhammad Garba ya dage zaman kotun har sai ranar 15 ga watan Yulin nan da muke ciki.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment