Tuesday, 9 July 2019

Shi'a: 'Yan sanda sun kama mana mutum kusan 100 a Abuja'

Rundunar 'yan sandan birnin tarayyar Najeriya, Abuja ta ce sun kama mabiya mazhabar Shi'a guda 40 yayin da suke gudanar da zanga-zangar da ta janyo tashin hankali a majalisar dokokin kasar.


Mai magana da yawun rundunar, DSP Anjuguri Manzah, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce mabiya Shi'ar sun yi kokarin shigaa majalisar da karfin tuwo inda jami'an 'yan sanda suka yi kokarin hana su.

Ya kara da cewa masu zanga-zangar sun harbi 'yan sanda guda biyu a kafa sannan sun yi amfani da duwatsu wajen raunata wasu 'yan sandan guda shida.


To sai dai Muhammad Ibrahim Gamawa daya daga cikin masu magana da yawun kungiyar ya musanta zarge-zargen 'yan sandan, inda ya ce ba su da makaman da 'yan sandan suka ce sun yi harbi da su.

Ya kuma kara da cewa sabanin mutum 40 da rundunar 'yan sandan ta ce ta kama musu, an "kama mana kusan mutum 100."

'Yan Shi'ar dai sun ce suna zanga-zanga ne kan ci gaba da tsare jagoransu Sheikh Ibrahim Elzakzaky da gwamnati ke yi wanda suka ya ce "yana cikin mummunan yanayin rashin lafiya".

Wasu ganau sun shaida wa BBC cewa an kona motoci a harabar majalisar, duk da cewa ba a fayyace wane bangare ne ya yi kone-konen ba.

Lamarin ya janyo an kulle dukkan kofofin shiga harabar majalisar dokokin.

Mabiya Shi'a dai sun dade suna kira da a saki jagoransu wanda hukumomin Najeriya ke tsare da shi tun shekarar 2015.

Irin wannan zanga-zangar ta sha janyo zubar da jini a kasar.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment