Monday, 8 July 2019

Shugaba Buhari ya gana da Amina J. Muhammad da Jagoran Libya

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari kenan a wadannan hotunan yayin ganawarshi da mataimakiyar sakataren majalisar Dinkin Duniya, Amina J. Muhammad a kasar Nijar inda shugaban yaje halartar taron kungiyar hadin kan kasashen Afrika ta AU.
A ganawar tasu shugaba Buhari ya bukaci kasashen Duniya da su taimaka wajan dawo da ruwan tafkin Chadi daya kafe wanda yayi sandin jefa miliyoyin mutane cikin halin haula'i.

Amina ta bayyana farin cikinta da amincewar shugaba Buhari yayi na yin kasuwancin bai daya tsakanin kasashen Afrika.
Shugaban ya kuma gana da jagoran hadaddiyar jam'iyyar kasar Libya, Fayez Al-Sarraf wanda ke shugabantar kasar, Buhari ya bashi tabbacin cewa Najeriya zata taimakawa kasar ta Libya wajan sake dawowa kan kafafunta.No comments:

Post a Comment