Tuesday, 9 July 2019

Shugaba Buhari ya yiwa wani Soja karin girma irin na Buratai

Shugaban Naieriya Muhammad Buhari, ya amince da karin girman Mejo Janar Lamidi Adeosun zuwa matsayin Lutanar Janar na gidan soji.


Wannan matsayi dai shi ne irin matsayin da Shugaban rundunar sojan kasan Yanzu Lutanar Janar T.Y Burutai yake rike da shi.

Wannan sanarwar ta fito a ta bakin kakakin rundunar sojan kasar nan, Colonel Sagir Musa ya sanya wa hannu.

Baya ga wannan nadi, shugaba Buhari ya amince da karin girman wasu manya sojoji guda 2 zuwa gaba.

Sojojin su ne
Brigadier General  Abdulmalik Biu, zuwa matsayin Major General, Abdulmalik ka fin karin girman shi ne General Officer Commanding 7 Division and Commander Sector 2 Operation Lafiya Dole Maiduguri

Baya ga haka an amince da karin girman Lieutenant AJ Danjibrin of 211 Demonstration Battalion Bauchi zuwa matsayin Captain 

Sagir Musa ya tabbatar da cewa, T.Y Burutai zai ci gaba da zama a mukaminsa na shugaban rundunar sojan kasar kasan nan a cewarsa.No comments:

Post a Comment