Tuesday, 9 July 2019

Shugaban majalisa yaje duba dansandan da 'yan shi'a suka jiwa rauni

Zuwan mabiyan shi'a majalisar tarayya a yau, Talata na daya daga cikin labarin yau da ya fi daukar hankula saboda zanga-zangar ta rikide zuwa tarzoma bayan da 'yan shi'ar suka kutsa kai cikin majalisar suka kuma lalata ababen hawa da gilasan tagunan ginin majalisar hadi da jiwa 'yansanda 4 rauni wanda har daya daga cikinsu ya mutu.A rahoton da Jaridar The Nation ta wallafa, ta bayyana cewa daya daga cikin 'yansandan dake cikin jini da kuma harbin bindiga a jikinshi ya bayyana cewa bindigar da aka harbeshi da ita ba ta gargajiya bace, kirar AK 47 ce.

Wannan hoton na sama kakakin majalisar Dattijanne, Femi Gbajabiamila da mukarrabanshi a yayin da ya kaiwa daya daga cikin 'yansandan ziyara a asibiti dan dubashi.

Rahotanni sun bayyana cewa an kama da dama daga cikin 'yan shi'ar sannan an jiwa da dama rauni.

Ga wasu hotuna daga yanda zanga-zangar ta yau ta kasance:
No comments:

Post a Comment