Wednesday, 31 July 2019

Shugaban Real Madrid ya fara dana sanin sayen Eden Hazard


Florentino Perez is not happy with Eden Hazard...
Ga dukkan alamu labari ya fara canjawa akan sayen Eden Hazard da kungiyar Real Madrid ta yi daga Chelsea inda dama tun ranar da ya fara atisaye a kungiyar wasu suka fara korafin cewa dan wasan yayi jiki.

A wancan lokacin dai wasu sun yi tunanin cewa hutun da dan wasan yajene yasashi yayi kiba haka, saidai har yanzu da ake buga wasannin sada zumunci, Hazard be murmure ba sannan be nuna bajintar azo a gani ba a kungiyar.

A wasan sada zumunci da Marida ta buga da abokiyar hamayyarta, Atletico Madrid ta sha kashi daci 7-3 sannan a wasan da suka buga da kungiyar Tottenham shima sun sha kashi da ci 1-0.

Har yanzu dai Hazard be ciwa Madrid kwallo ba.

Watakila wannan daliline yasa tuni har shugaban kungiyar ta Real Madrid, Florentino Perez ya fara dana sanin sayen Hazard din kamar yanda Sport suka ruwaito.

Labarin yace dama dai Perez ya kawo Hazard ne dan ya farantawa kocin kungiyar, Zinedine Zidane rai, bawai dan yana son dan wasan ba.

Abindai jira a gani shine fara kakar wasa, a nanne za'a tantance ko kwalliya zata biya kudin sabulu akan saye  Hazard din. A tsohuwar kungiyarshi ta Chelsea dai Hazard ya bar tarihi me kyau na yiwa kumgiyar bajintar azo a gani.

Sannan Hazard ne dan wasa mafi tsada da Madrid din ta taba siya a tarihinta inda ta sayeshi akan fan miliyan 130.


Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment