Sunday, 21 July 2019

Sojan Sama Ya Tsince Kaminin Naira Milyan 15 Ya Mayarwa Mai Shi

SOJAN SAMA MUSULMI YA YI ABIN A YABA
Rundinar sojin saman Nijeriya za ta sakawa wani jami'inta mai suna Aircraftman Bashir Umar wanda ya tsinci kudi Euro dubu talatin da bakwai (€37,000) kimanin naira miliyan goma sha biyar da dubu hamsin da tara (N15,059,000) a filin jirgi, kuma ya mayar da kudin zuwa ga mai shi.


Kamar yadda rundinar sojin saman Nijeriya ta fitar da sanarwa ta bakin kakakinta Air Commodore Ibikunle Daramola, tace wannan jami'in nata Bashir Umar ya tsinci kudin ne ranar talata 16-7-2019 a sansanin mahajjata lokacin da suke bada tsaro a filin tashi da saukar jiragen sama na Malam Aminu Kano tare da abokan aikinsa.

Lokacin da Bashir ya tsinci kudin, sai ya tarar da akwai nambar wayan mai kudin, nan take ya kira mai kudin sunansa Alhaji Ahmad ya ba shi abinsa.

Bayan da shugaban sojojin saman Nigeria Air Marshal Sadik Abubakar ya samu labarin abinda jami'in sa yayi, sai ya umarci mai lura da tsare tsaren gudanarwan rundinar sojin saman Nijeriya da ya yi gaggawa kyautata wa wannan jami'i, domin hakan ya zama abin koyi ga sauran jami'ai.

Bashir Umar ya kare mana martaban addinin musulunci, kuma ya kara fito da darajar musulunci da kuma rundinar sojin saman Nigeria, hakika wannan jami'i 'dan uwa matashi ya kamata ya zama abin koyi, tabbas ya cancanci a masa karin girma, kuma a bashi lambar yabo.

Muna rokon Allah Ya tsareshi, Ya daukaka darajarshi, Ya saka masa da mafi alherin sakamako. Amin.
Datti Assalafy.


No comments:

Post a Comment