Sunday, 14 July 2019

Sojiji 5 sun tsere da biliyoyin kudi na me gidansu

Rahotanni sun bayyana cewa wasu sojoji 5 sun kwacewa ogansu biliyoyin kudi sannan suka ajiye bindigu da kayan aikinsu suka kama gabansu.Premiumtimes ta bayyana cewa, ta samu labari daga wata majiya ta rundunar sojin Najeriya cewa sojan da akawa fashin shine Hakeem Otiki dake kula da runduna ta 8 ta sojin Najeriya dake Sakkwato.

Kudin na babban sojan ne da ya umarci sojojin rakasu zuwa Abuja saidai ba'a bayyana inda za'a kaisu ba.

Sojin sun raka kudin zuwa Jaji Kaduna, daga nanne suka kwace kudin suka ajiye kakinsu da bindigoginsu suka kama gabansu.

Ba'a bayyana yawan kudin ba amma wasu rahotanni sun bayyana cewa sun kai biliyoyin Naira.

Wata majiya ta bayyana cewa sojojin sun kwaci kudinne rashin kulawa dasu da hakkokinsu sannan suna ganin ana wadaka da makudan kudi.

Hukumar soji ta bayyana neman sojojin ruwa a jallo.

Cikin sojojin akwai, Gabriel Oluwaniyi, Mohammed Aminu, Haruna, Oluji Joshua da kuma Hayatudeen Abubakar.

Rahoton yace sojojin sun dade suna karantar harkokin ogannasu.

No comments:

Post a Comment