Thursday, 11 July 2019

Sunayen Sabbin ministocin shugaba Buhari


Labarai na yau dake fitowa daga jaridar The nation na cewa 12 zuwa 15 cikin tsaffin ministocin shugaban kasa, Muhammadu Buhari zasu sake samun mukamin nasu.

Sunayen ministocin kamar yanda labarai suka bayyana tuni har sun kai ga hannun kakakin majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawal, saidai babu tabbacin hakan.

Dokar kasa dai ta baiwa shugaban kasa dama ya nada ministoci 36 zuwa 42. Kuma labarai na nuna cewa, shugaban na son ci gaba da tafiya da wasu daga cikin ministocin saboda bajintar da suka nuna.

Labarai dai daga The Nation din sun ci gaba da cewa, ministocin da ake sa ran zasu sake komawq kan mukamansu sune, ministan shari'a, Abubakar Malami ( SAN), ministan Ilimi, Adamu Adamu, ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, Ministan Kudi, Zainab Ahmad, ministar harkokin mata, A'isha Abubakar, ministan watsa labarai, Lai Muhammad, ministan ayyuka, wuta da gidaje, Babatunde Fashola, ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ministan Abuja, Muhammad Musa Bello, ministan Albarkatun ruwa,Sulaiman Adamu Kazaure, Ministan kimiyya da fasaha, Ogbonnaya Onu, ministan wasanni, Solomon Dalung. Dadai sauransu.

Ibe Kachikwu, tsohon gwamnan Osun, Ogbeni Rauf Aregbesola, Tsohon gwamnan Legas, Akinwunmi Ambode suma ana sa ran zasu samu mukamin amma dai babu tabbaci akansu, kamar yanda Labarai suka nuna.

No comments:

Post a Comment