Friday, 12 July 2019

Talauci ya karu a Najeriya>>Bincike

Rahoton majalisar dinkin Duniya ya bayyana cewa talauci ya karu a Najeriya cikin shekaru 10 da suka gabata inda yawan talakawan Najeriya suka karu daga miliyan 86 zuwa miliyan 98 daga shekarar 2007 zuwa 2017, kamar yanda labarai na yau suka nuna.Binciken da bangaren kula da ci gaba ta majalisar dinkin Duniya da hadin kan jami'ar Oxford suka gudanar ya nuna cewa a takarda da kuma gwamnatin tarayya, bincike ya nuna cewa talaucin da ake fama dashi be canja ba cikin shekaru 10 da suka gabata amma a zahiri idan aka shiga jihohi da kananan hukumomi za'a ga cewa talaucin ya karu, kamar yanda sakamakon binciken da aka fitar jiya, Alhamis ya nunar.

Labari da jaridar Punch ta ruwaito ya ci gaba da cewa, akwai kuma tazara me yawa tsakanin masu kudi da talakawa musamman a kasashen dake da matsakaicin arziki da kuma talakawa wanda hakan dalilin rashin daidaiton wadata ne tsakanin kasashen kai harma da cikin gidaje da ake fama dashi.

No comments:

Post a Comment