Friday, 19 July 2019

Uba yawa diyarshi fyade dan tabbatar da budurcinta

Wani mutum me shekaru 37 daga Oyo me suna, Wasiu Orilonise ya yiwa diyarshi me shekaru 15 fyade inda ya bayyanawa kotu cewa yayi hakanne dan ya tabbatar da budurcinta sannan kuma ya bata kariya.Mahaifin ya ci gaba da gayawa alkalin kotun magistre dake Oyo cewa tun bayan da ya rabu da matarshi, shine ke kula da 'ya'yanshi kuma ya farawa diyar tashi fyadene bayan da ya bincike ta ya gano cewa bata rasa budurcinta ba.

Ya kara da cewa yakan yi mata fyade da dare da kuma da safe kamin ta tafi makaranta saidai ya roki kotu data yafe mai.

Alkalin ya bayar da umarnin tsare mahaifin a gidan kaso inda ya daga sauraren shari'ar zuwa 30 ga watan Yuli.

No comments:

Post a Comment