Wednesday, 10 July 2019

Wutar lantarki ta kashe mutum biyu dake aikin saka fitilar kan hanya

Wadannan hotunan wasu bayin Allahne da wutar lantarki ta yi sanadin mutuwarsu jiya, Talata a kan titin zuwa matatar mai dake garin Kaduna.Rahotanni sun bayyana cewa shedun gani da ido sun bayar da labarin, mutanen na aikin saka irin fitilar kan titinnanne sai wayar wutar lantarki ta taba karfen da suka yi tsani dashi, dalili  fadowarsu suka mutu kenan.

Bayan faruwar lamarin, an sanar da 'yansanda suka kawo dauki.

No comments:

Post a Comment