Tuesday, 2 July 2019

Yadda Bilkisu Ta Rafke Mijinta Har Lahira Saboda fita ba tare da izini baWata matar aure mai suna Bilkisu Isah ta hallaka mijinta, Isah Egba, yayin da suke fada a Anguwar Sabon Tasha, garin Abaji na birnin Abuja.

Wani makwabcinsu mai suna Salihu ya bayyana cewa rikicin ya abku a ranar Alhamis da misalin karfe 9:12 na dare sakamakon sabani da ya shiga tsakanin mamacin da matarsa mai 'ya'ya biyar.

Ya ce mamacin ya tuhumi matarsa a kan fita daga gidan ba tare da yardarsa ba. Da matar ta dawo gida da misalin karfe takwas na dare sai mijin ya kore ta daga gidan.

Salihu ya kara da fadin cewa, mijin nata ya dirar mata cikin fushi tare da tura ta wajen gidan. Ita kuma cikin fushin abin da mijin nata yai mata sai ta rarumi wani icce ta maka masa.

Ya ce, nan take mijin ya yanke jiki ya fadi kasa yana zubar da jini. Hakan ya sanya wasu makwabta suka ruga da shi asibitin 'Abaji Comprehensive Health Centre' inda daga baya suka tura su asibitin koyarwa na jami'ar Abuja da ke Gwagwalada. Amma cikin ikon Allah sai ya rasu da tsakar daren ranar Juma'a.

Jaridar City News ta bayyana cewa an binne mamacin, wanda yake ma'aikaci a sashen kudi na sakatariyar Abaji, kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar. Limamin babban masallacin JIBWIS, Malam Muhammad Tauheed, ne ya yi masa sallah. 

Kakakin rundunar 'yan sandan birnin Abuja, DSP Anjuguri Manzah, ya tabbatar da afkuwar abin, inda ya ce 'yan sanda suna kan bbincike
Sarauniya.

No comments:

Post a Comment