Sunday, 14 July 2019

'YADDA MUKA YI DA WATA 'YAR MADIGO'


Wani dan jarida me suna Mubarak Umar ya bayar da labarin yanda ya hadu da wasu 'yan mata masu madigo. Ya bayar da labarin nashine a shafinshi na Twitter inda ya fara da:

'YADDA MUKA YI DA WATA 'YAR LESBIAN

Ban so bada labarin nan ba, amma wani yanayi ya sani zan yi tsokaci kan bala'in lesbian da yadda wasu mutane har da wadanda ke wakiltarmu a Majalisar Dinkin Duniya suke kokarin ganin lallai sai an bawa kowane jinsi damar auren a juna.

Haduwa muka yi da wasu 'yan mata a wani garden haka...sai hira ta shiga tsakanin mu, domin daya daga ciki ta yi bala'in birge ni, ba don tana da kyau ba, sai don yadda a wurin kusan yana walwala da zirga-zirga, amma ita tana gefe zaune, sai kawai ta yi murmushi.

Ina gefe ni da wani friend dina kowa hannunsa rike da Chapman muna sha, sai na ce masa "gaskiya yarinyar can mai shuru-shuru ta birge ni, zan iya yi mata magana fa".

Muka yi dariya tare, bayan wasu 'yan lokuta abokin nawa ya wuce ya bar ni. Sai na ga bari in gwada sa'a.

A hankalin na tunkari inda take zaune, na yi mata murmushi da murgujejen bakina. Ta mayar min da murmushi irin mai tayar da tsikar jikin namiji. Nan na ji wani sanyi a raina, na fara tunani da alamu na samu shiga.

Na yi mata kafin na nemi wuri na zauna. Sannan na ce gaskiya kin birge ni kawai, shi ya sa na ga dacewar in yi miki magana, ba don wani abu ba. Ko da kuwa daga nan ba zan kara ganin ki ba.

Kawarta da ke gefe kadan (dama na gan su tare ne tun da farko), ta zo wurin da sauri ta "ce sannu bawan Allah, lafiya dai...?"

Na ce "lafiya kalau, magana na zo in yi da kawarki"

Ta ce, "wace irin magana kenan?"

Na kalli wancan da ta yi min, sannan na kalli kawar...

"Na dauka kin ji me na ce. Kawarki ta birge ni, shi ya sa na zo in yi magana da ita." Na ce da ita.

Sai kawar ta yi murmushi ta ce, "Amma ba ta fada maka cewar she is my girlfriend ba?"

Na dan yi dariya, "to ai ko uffan ba ta ce min ba kika zo kika karbe zance."

"she is my girlfriend" ta ce da ni...

Kamar in yi dariya, Amma na basar don ina son gane me take nufi da kalmar 'girlfriend'.

"Baiwar Allah, ban gane me kike nufi ba, yi min dalla-dalla don gane." Na ce da ita.

Sai ta ce, "ka taba yin budurwa?" 

Na gyada kai alamun eh.

Sai ta ce, "to shi ne abinda nake nufi. Wannan budurwata ce" ta fada da Hausa.

Wani irin kallon na yi yarinyar da ta yi min din domin tabbatar da zancen kawar tata. Shirun da na gamu da shi shi ya tabbatar min da cewa lallai maganar waccan gaskiya ce.

Gaba daya sai hankalin ya koma kan kawar. Na karkato da kujerata yadda zan fuskance ta sannan na ce. "Yanzu kina nufin a matsayin ki na mace, sai kuma ki ka yi budurwa mace, duk tarin mazan ke duniya?"

Shiru ta yi ba ta ce komai ba, hakan ne ya ban damar ci gaba da zuba.

"To amma don Allah ba ki ji kunyar budar baki ki fada min wannan maganar ba." Shi ne kalmar da ta fito daga bakina.

"Hmmm!" Ta fara yi kafin ta ce, "ni dai ba wa'azi za ka yi min ba. Tunda na fada maka yadda muke da ita, sai ka koma wurin zamanka, ka ci gaba da sha'aninka.

Nan take na yanke hukunci yin aikina na jarida... Tambayar qwaqwa.

Sai na juya kan wadda na fara yi wa magana tunda farko. "Ke yanzu kina mace, sai ki bari wata mace ta rika fadar irin wadannan kalamai a kanki?"

Murmushi ta yi kawai...

Caraf dayar ta karbe, "ka ga Malam, ka kyale mu kar ka canja mana 'mood' dinmu." Ta ce da ni.

Na kyal-kyale da dariya na ce, "au har wani mood kuke shiga? Ban son iskancin ba. Yanzu don Allah kina mace sai ki haye ruwan ciki 'yar uwarki? To me za ki fahimta?

"Ni ban ce maka komai ba. Ka ga tunda muka zo wurin nan, Babu wanda ya tunkari my girlfriend ya ce zai yi mata magana sai kai. Ka Yi, kuma ka tabbatar ba ka da wuri, sai ka tafi." Ta ce.


Na yi tagumi da hannu biyu ina kallon su daya bayan daya. Sannan ce da kawar "to ai kawai sai ki aure ta. Tunda kin hana ta kula maza."

"Wai kai wane irin mutum ne? Don na ce maka kawai sai ka kawo maganar aure. Ai matsalar ba za mu iya haihuwa. Wata rana kuma zan so haka."

Dariya na yi irin ta Basawa India. Na ce, "kin san ba za ki iya yi mata ciki. Amma kina binta kamar wata mijinta. Kin hana kowa kula ta. No wonder na ga ko walwala ba ta yi a nan, so ashe ke ce kike hana ta.


"Kuna yaudarar kanku da sunan wayewa ko 'yanci dan'adam. Kun kirki abinda ku kanku kun san ba zai amfane ku a duniya ba, balle kuma lahira. Kawai ki bar min yarinyar nan in jarraba sa'a."

Na cika da mamaki da na ji ta ce, "ko ka jarraba ba za ka yi nasara ba. Don ban son namiji.


Kalaman yarinyar sun yi matukar bani mamaki. Sun nuna tana jin dadin rayuwar 'yancin da suke ikirari. Shi ya sa ita ma ta tabbatar min tana son zama da mijin tata (afuwan). Haka suka ce.

Yo ni da ko namiji ba na shakka, Ina ji ina gani mace ta kasa ni a wurin mace.


Kuma abin haushi wata rana tana so ta auri namiji domin ta samu haihuwa. Tana da yakinin babu yadda za a yi a bar ta ta auri mace 'yar uwarta.

Na bar wurin bayan na basu labarin Elisa & Marcela, yadda suka yi auren jinsi na farko a kasar Spain da irin wahala da suka sha.


Ni na zaci 'yan qwaqulen nan sun yi sallama da maza, shi ya sa sam ban cika damuwa da lamarinsu ba. Ashe cikin zuciyar su akwai so, qauna da burin auren maza wata rana.

To ina matsalar take?'
No comments:

Post a Comment