Wednesday, 10 July 2019

Yadda Na Kama Matata Tana Tura Wa Samarinta Hotunanta Na Tsiraici>>Mutumin Da Matarsa Ta Daba Wa Wuka A Kano

Daga karshe dai Sa'id Hussain, wanda matarsa 'yar shekara 21 mai suna Fatima Musa ta kusa kashewa bayan ta daddaba masa wuka, ya samu saukin ciwukan, inda ya bayyana ainahin abin da ya shiga tsakaninsa da matarsa. 


Rikicin ya faru da misalin karfe daya da rabi na daren Juma'a, watan Yuni, a cikin gidan ma'auratan da ke unguwar Mai Kalwa, Na'ibawa, karamar hukumar Kumbotso, jihar Kano.

Lamarin ya jawo cece-kuce da mahawara mai zafi a kafofin sada zumunta, inda wasu suka daura laifin a kan mijin, wasu kuma a kan matar.

Yayin da wasu suka zargi Sa'id da lakada wa matarsa dukan tsiya, wanda ya tursasa wa Fatima daba masa wuka domin kare kanta, wasu kuma sun zargi Fatima da laifin bin maza da rashin biyayya ga mijinta.

Amma a nata jawabin, Fatima, daliba a fannin karatun lauya a jami'ar Bayero, ta zargi mijinta da ritsa ta a cikin dakin dafa abinci, inda ya dinga jibgar ta duk kuwa da cewar tana dauke da juna biyu. Hakan ya sanya a cewarta ta daba masa wuka a cikin yunkurinta na kare kanta. 

A cikin wani bidiyo da ya watsu a kafafan sada zumunta, Fatima ta nuna wasu ciwuka a goshinta, fuskarta, hannayenta da wasu sassa na jikinta, inda ta ce mijin ne ya ji mata ciwukan a lokacin da yake dukanta. 

Sai dai a ranar Litinin, Sa'id, wanda ya samu sauki daga ciwukan da ya ji a gefen cikinsa da hannuwansa, ya yi taron manema labarai a gidansa, inda shi ma ya bayyana nasa bangaren labarin, kamar yadda DAILYFOCUST ta rawaito. 

"Na kama matata tana rawa mara kyau a cikin falona inda take rikodin din rawar a wayarta tare da tura wa samarinta. Na gaya wa mahaifiyarta abin, inda ita kuma ta tambaye ni kan ko yayar matata da kakarta sun san abin da ke faruwa, sannan ta roke ni kan kar na gaya wa kowa domin kare martabar gidansu. 

"Bayan nan na kalubalanci daya daga cikin samarin da matata take musayar sakon murya (Voicemail) amma ya ce min shi sam bai san tana da aure ba. Wannan shi ne daya daga cikin sakonnin voicemail sama da 30 da na samu," ya fada a lokacin da ya kunna wata tattaunawa da ya yi da daya daga cikin wadanda yake zargin samarinta ne a wayar iPhone. 

"Ina kuma da shedar yadda matata ta gayyato wani masoyinta daga Abuja inda ta zauna da shi a wani hotel a Bompai da ba zan bayyana sunanshi ba. Ta aikata hakan a ranar 26 ga watan Afrilu, 2016, alhali tana da aure. Ta je hotel din da misalin karfe 10:13 na safiya sannan ta zauna a can har zuwa 12:16 na rana. Sannan na'urar daukar hoto ta tsaro (CCTV) da ke cikin hotel din ta dauki wannan bayanin da nake.

"Sannan a wannan ranar ta Juma'a, na kama ta tana shan kwayoyi a gidana. Tana shan shisha da wasu abubuwa masu dauke da sinadarin nicotine mai matukar karfi. A azimin karshe na Ramadan, ta yaryada maganin kwari mai dauke da guba a cikin abincina, soyayyan kwai. 

"Matsalar haka ta yi tsamari da har ta sa muka nemi ganin Dakta Bashir Umar, babban limamin Masallacin Juma'an Al-Furqan, wanda yake mai bayar da shawarwari a kan matsalolin aure domin ya ba mu shawarwari.

"Mun je gurin Dakta Bashir tare da matata, mahaifiyarta da yayanta a cikin motata. Na bayyana dukkan zargin da nake mata ciki har da lalata da maza da shan kwayoyi, wadanda kuma ta yarda da ta aikatan hakan ga Dakta Bashir. 

"Amma a wannan ranar ne dai bayan mun dawo gida ta daba min wuka bayan na kwace wayarta wadda take tura wa samarinta hotunanta da bidiyonta na tsiraici. Na riga na kwanta a lokacin da ta dauko wukake guda biyu daga dakin dafa abincinta ta zo dakin. Ta zauna a gaban gadona, bayanta na fuskantar madubi tamkar tana yin tunani mai zurfi. A lokacin ta daga wukar farko ta buga min a gefen cikina sannan ta jefe wukar bayanta. 

"Na farka firgigit inda na ga ta daga dayar wukar za ta daba min. Na yi kokarin rike hannunta, inda a cikin haka na ji ciwo. Wannan shi ne tabon kamar yadda kuke gani. 

"Ta kuma daga wukar za ta daba min amma an goce, wanda ya sa wukar ta nutse a cikin katifa. A lokacin na mike na rike hannunta domin na kwace wukar. A hakan ta gatsa wa hannuna cizo, inda take gargadina da in saki. A wannan gwagwarmayar na hankada ta ta fadi, kanta ya bugi gefen dirowa sannan ta fada dandabaryar kasa, wanda ya sa fuskarta ta kumbura.

"Ba gaskiya ba ne wai mun yi fada a dakin dafa abinci. In an duba za a ga shatin jini kawai daga kasan dakina zuwa falo. 

"Saboda haka, ina kalubalantar danginta na dukka bangaren uwa da uba da su kawo kowacce irin sheda da ta nuna cewar kullum ina dukan 'yarsu. Hotunan bidiyon da ke kewaye na wannan rikicin da muke fada ne. 

"Cikin taimakon Allah abokina Lawali ya ceci rayuwata a ranar ya kai ni asibiti. A lokacin da yake rike da kafata yayin da nake birgimar radadi, fuska ta uku da na gani a kaina ita ce ta surikata. Nan take na gargade ta da kada ta taba ni. Abokina Ustaz zai iya yin shaidar haka. 

"Na koka mata a kan tana sane da halayyar matata ta bin maza da kuma yunkurin da ta yi na sanya min guba a abinci amma ba su dau mataki ba. Daga jin haka sai surikata ta fara min nuni da in yi shiru, tana roko na da kar in fallasa wa duniya mummunar halayyar 'yarta.

"Kafin in bar asibiti, surikata ta nemi izni a gun abokina Ustaz na ta hadu da 'yarta tare da tattaunawa da ita cikin sirri. 

"Akwai wani kes iri daya da wannan a Abuja wanda mijin ya mutu. Hakan ya sanya surikata ta hada kai da 'yarta kan su lalata dukkan wata sheda tare da daukar nauyin yakin bata min suna a kafofin sada zumunta. 

"Sun dauki nauyin hotunan bidiyo da wasu hanyoyi wanda aka zarge ni da shan giya, shan kwayoyi da dukan mata. An aikata hakan domin a bata min suna tare da sanya wa a kalleni a matsayin mugu, domin duniya ta tausaya mata. Amma ina da shedu a kan halayen alfasha, rashin biyayya da shan kwayoyi da take yi," Sa'id ya fada. 

Da aka tanbaye shi a kan ko ya taba kai wa gidansu karar halayyar da yake zarginta da aikatawa sai ya ce:

"Na sha kai kararta gurin iyayenta. Kuma duk lokacin da na sanar wa da gidansu, ina tura shedar abin da ta aikata ta yanar gizo. Ina tura wa mahaifinta da mahaifiyarta shedar ta Whatsapp. Idan ba su da kwafin abin da na tura masu, ni ina da su a nan. 

"Wadannan wasu ne daga cikin hotuna tsirara da bidiyo da take yi tana tura wa samarinta, alhali kuma tana da aure," Sa'id ya fada alokacin da yake nuna wasu bidiyon matarsa a wayar iPhone domin karfafa hujjarsa. 

"Amma martanin iyayen shi ne in taimaka in rufe su, in barsu a gurina, ka da in fallasa su domin zan bata masu suna. Matata har tana musayar fina-finan batsa da wasu daga cikin kawayenta." 

Sa'id ya kuma yi ikirarin cewa bai taba sanin matarsa ba mutuniyar kirki ba ce kafin ya aureta, kuma bayan ma ya aure ta bai gano halayayyar da take aikatawa da wuri ba saboda ba ya duba wayarta. 

Ya ce duk da ya gano abin da take aikatawa, bai yi yi yunkurin sakinta ba saboda a ko da yaushe iyayenta na bashi karfin gwiwa a kan za ta canja, kuma shi ma ya yi ta yi mata addu'a a cikin watan azumi na Allah ya gyara ta.
Sarauniya.


No comments:

Post a Comment