Sunday, 14 July 2019

Yadda Na Zama Kanal Din Soja Daga Almajiranci, Cewar Jigon Kungiyar Izala, Sheik Adamu Girbo

"Ni tsohon soja ne mai mukamin Kanal. Na yi aikin soja tsawon shekara 35 kuma na shiga aikin soja ne lokacin da aka sanya ni a makarantar allo, lokacin ina fadar Mai martaba Sarkin Gombe. A lokacin ana Yakin Basasa (Yakin Biyafara) aka zo ana neman sojoji masu sana’a, ni kuma na iya tuka babbar mota, har Bature ya ba ni lasisin tuki, sai aka dauke ni a matsayin kurtu direba a 1967.


Da shiga ta soja sai muka tafi filin yaki, muka gwabza Yakin Biyafara na shekara daya. Bayan yaki ya kare sai muka  dawo Kaduna. Da yake babbar mota nake tukawa kuma aikinmu ba koyaushe ba ne, iyakaci mu je Legas mu dauko kayan yaki masu nauyi, don haka muna iya yin watanbiyu zuwa uku muna zaune ba mu je ko’ina ba. Wannan zaman da muke yi ne ya ba ni dama na yi ta karatu a gida, irin karatun zauren nan har na sauke Alkur’ani a wajen wani mutumin Zariya mai suna Malam Muhammadu. 

A yawon karatun da nake yi ne har na hadu da Sheikh Abubakar Mahmud Gumi. Ina karatu a gabansa har muka hadu da Sheikh Isma’ila Idris Zakariyya Jos, shi ma yana karatu a wajen Gumi. Ganin cewa ni soja ne sai Abubakar Gumi ya karfafa mini gwiwar yin karatu, inda ya ce me ya sa ba zan samu wata makaranta in shiga ba? Sai na ce masa ai gidan soja ba za su bari ba. Hakan ya sa ya rubuta takarda ya tura wa Runduna ta Daya, ya roke su a kan su tura ni wajen Limamin Soja wanda hakan zai ba ni dama in tafi karatu.

 Da damar ta samu bayan yaki ya kare ina zaune a Kaduna, sai na tafi Katsina Teachers’ Collage a 1976, na yi Higher Islam, lokacin ana kiran makarantar H.I.S. na yi shekara 4, kafin in dawo Kaduna Kungiyar Izala ta fito kuma sai na samu kaina a ciki. Saboda ni da Isma’ila Idris mun yi karatu tare a wajen Gumi sai ya zama muna da dangantaka ta ilimi muna hulda, ana taron kafa kungiyar a tsakanin  1976 zuwa 1979. Ni kuma na gama makaranta a 1980, da na dawo sai soja suka gane cewa na zama dan Izala. A lokacin Shugaban Limaman Soji, dan Darikar Tijjaniya ne, hakan ya sa muka samu matsala, ya rasa yadda zai yi da ni; a tunaninsa duk inda ya kai ni zan yada Izala. Wannan ya sa na zauna na wasu watanni sai ya ce in je in nemo wata makaranta zai bar ni ina tafi. A lokacin sai na gamu da wani mutumin Gombe, Bappah Muhammad Umar, ya sama min izinin shiga Kwalejin Koyon Aikin Shari’a ta Misau a Jihar Bauchi. 

Na yi shekara uku, na samu Diploma sai aka mayar da ni wani gari gaba da Kalaba mai suna Abaka, Bataliya ta 41. Ni nake limanci, daga baya muka samu matsala sai aka dauke ni a wajen, aka mayar da ni Bataliya ta 31 a garin Takum a Taraba. Duk da haka da aka ga na dawo Arewa kuma duk inda Izala take wa’azi da ni ake yi a Takum da Ibbi da Donga, sai abin ya dame su, sai aka kira ni Legas don a yi min intabiyu, za a ba ni anini daya; lokacin kuma igiyata biyu ce (Kofur)".
Rariya.


No comments:

Post a Comment