Pages

Wednesday 17 July 2019

Yadda Wani Matashi Ya Kirkiri Injin Walda Ta Amfani Da Ruwa Cikin Bokiti A Faskari

Wani matashi kuma shugaban Cibiyar  'Uzairu Aliyu Foundation Entrepreneur Do It Yourself' Muhusin Aliyu Faskari ya hada wani injin din yin walda da ake amfani da botikin roba da kuma  ruwa a cikinsa ya fitar da wutar yin walda mai karfin gaske.


A lokacin da nake zantawa da shi ya ce man " ita wannan fasahar mun samo ta ne domin samar wa masu walda sauki wajen daukar injin din walda in za su fita aiki zuwa cikin gida, ko wani wajen da ba inda suke sana'ar waldar ba.

" Sannan ga saukin cin kudi ko mai karamin karfi ba zai gagare shi ba, sannan zai fitar da wutar walda wadda injin din walda ba zai iya fitar da ita ba, sannan komin karfin karfe za ta gasa shi sosai ta walde shi cikin sauki da sauri." Inji Injiniya Muhsin Aliyu

Da na tambaye shi ko inda wasu sun gani sun kuma yi sha'awar suna bukata a yi masu ya za su yi? Sai ya ce; " Ina nan a cikin garin Faskari da ka shiga garin ka nemi wanene Injiniya Muhsin Aliyu Faskari za ai maka kwatance da inda nake, sannan kuma mai bukata zai iya tuntuba ta ta layin wayata 07037783135"

Kirkire-kirkire da kawo sabbin fasahohi na daya daga cikin ababen dake kawo wa kasa ci gaba a duniya har ta zama abin kwatance kamar kasar China.
Rariya.


No comments:

Post a Comment