Sunday, 14 July 2019

'Yan bindiga sun kashe kawun Sanata Elisha, da garkuwa da matar mahaifinsa

'Yan bindiga sun kashe kawun Sanata Elisha Abbo kuma sun yi garkuwa da matar mahaifinsa a ranar Asabar.


Sanata Abbo, wanda shi ne dan majalisar dattawa mai wakiltar Adamawa ta Arewa ya shaida wa BBC cewa dan uwansa ne ya kirashi ya shaida masa abin da ya faru.

Sanatan ya ce: '' 'yan bindigar sun zo gidana ne tsakinin 12:30 na rana zuwa 1:00 na ranar Asabar dauke da bindiga samfurin AK-47 inda suka dauke matar mahaifina.''''Kanin mahaifina ya fara kwarmata ihu ke nan sai suka harbe shi.''

Sanata Abbo ya ce ya shaida wa kwamishinan 'yan sandan jihar yadda wannan lamarin ya faru.

Sai dai 'yan sandan sun bayyana cewa suna gudanar da bincike domin ganin cewa sun gano masu hannu a wannan harin.

Har yanzu dai akwai sauran rina a kaba dangane da batun garkuwa da mutane da kuma kai hare-hare musamman a arewacin Najeriya.

Ko a ranar Juma'a da daddare sai da 'yan bindiga suka harbe Funke Olakunrin, mai shekara 58, wadda 'ya ce ga Shugaban Kungiyar Yarabawa ta Afenifere, Chif Reuben Fasoranti.

Sanata Abbo wanda shi ne mai mafi karancin shekaru a majalisar dattawa ta tara a Najeriya ya shiga rudani a 'yan kwanakin nan tun bayan da jaridar Premium Times ta intanet ta wallafa wani bidiyo mai tsawon minti 10 da ke ikirarin nuna sanatan yana dukan wata mata a cikin wani shagon sayar da kayan wasan jima'i.

Sai dai sanatan ya fito ya roki gafarar matar da 'yan kasar dangane da wannan lamari da ya faru. Sannan kuma ya bayyana a gaban wani kwamiti da majalisar dattawan ta kafa domin ya binciki lamarin.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment