Tuesday, 9 July 2019

'Yan shi'a sun kutsa kai cikin majalisar tarayya, Sun faffasa gilasan tagogi, sun jiwa 'yansanda 3 rauni

A yau Talata mabiya Shi'a sun yi zanga-zanga a majalisar tarayya inda ta koma zuwa tarzoma. 'Yan shi'an dake zanga-zangar neman sakin shugabansu, Ibrahim Zazzaky sun kutsa cikin majalisar ta hanyar haura kofar farko.Rahotanni daga kamfanin dillancin Labaran Najeriya, NAN sun bayyan cewa 'yan shi'an sun kutsa cikin majalisar da karfin tsiya sannan kuma suka faffasa gilasan tagogin majalisar dana motocin jami'an tsaro da masu ziyara da abin aya ritsa dasu.

Hakanan rahoton yace, sun jiwa 'yansanda 3 rauni wanda yanzu haka suna asibitin majalisar suna karbar magani.

Saidai jami'an tsaro sun rufe kofar majalisar ta biyu inda suka hana shiga da fita.

Kuma rahoton yace har yanzu 'yan majalisar na ciki ana zaman majalisa kamar yanda aka saba.

No comments:

Post a Comment