Thursday, 11 July 2019

'Yan shi'a sun sake fitowa zanga-zanga a Abuja: 'Yansanda sun tarwatsa su

Labarai na yau na nuni da cewa an sake samun arangama tsakanin 'yansanda da 'yan shi'a masu zanga-zangar gwamnati ta saki shugabansu, Shiekh Ibrahim El-Zakzaky da take tsare da shi.Labarai na cewa, lamarin ya farune a gaban sakatariyar gwamnatin tarayya dake babban birnin tarayya,Abuja inda 'yansanda suka yi harbi a iska tare da harba barkonon tsohuwa dan tarwatsa 'yan shi'ar.

Jama'a da dama sun tsorata da wannan alamari inda suka rika neman mafaka.

'Yan shi'ar sun sake haduwa suka yi wani sabon gangami dan cu gaba da zanga-zangar.

No comments:

Post a Comment