Sunday, 14 July 2019

Yanda muka hana majalisar tarayya tsige Obasanjo>>Janar Yakubu Gowon

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Janar Yakubu Gowon ya bayyana yanda suka tseratar da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo daga tsigewar majalisar tarayya ta lokacinshi.Gowon ya bayyana hakane a wajan wani taron da akayi kan ci gaban Najeriya inda yace, a wancan lokacin shi da wasu 'yan Najeriya masu muradun ci gaban kasarnan da dorewar Dimokradiyya suka samu kakakin majalisar dattijai na wancan lokacin, Pius Anyim da na majalisar Wakilai, Ghali Umar Na'abba inda suka rokesu akan kada su tsige Obasanjo.

Yace sun yi wancan yunkurine dan kare sauran shuwagabanni da zasu zo bayan Obasanjo inba dan haka ba da suma sai sun gamu da irin wannan matsalar, injishi.

Yace kuma saboda girmansu da shuwagabannin majalisar ke gani sai suka hakura da tsige Obasanjon.

No comments:

Post a Comment