Saturday, 13 July 2019

Yaro ya haye saman gidansu dan gudun Kaciya

Wannan hoton wani yarone dan kasar Indonesia da aka zo mai kaciya amma saboda tsoro ya haye saman gidansu ya ki saukowa. Likitan da zai mai kaciyarne, Anik Sutari ya wallafa wannan labari a shafinshi na facebook da kuma ya dauki hankula sosai.


Likitan yace yanawa yara da yawa kaciya amma bai taba ganin wanda aka sha irin wannan dambarwar dashiba. 

Iyayen yaron sun yi iya yinsu dan ganin an sauko dashi daga saman amma yakiya, dole aka kyaleshi dan gudun kada wani yayi yunkurin hawa ya tsoratashi ya fado.

Daga baya sai malamin makarantar yaron aka kira shima da kyar ya samu ya sa yaron ya sauko daga sama.

Yara kan kai shekaru 5 kamin a musu kaciya a kasar Indonesia.
No comments:

Post a Comment