Tuesday, 9 July 2019

Za mu farfado da matatun man Najeriya kafin karewar 2023>>Kyari

Sabon shugaban kamfanin albarkatun man Najeriya NNPC, Mele Kyari, ya sha alwashin gyara dukkanin matatun man kasar, kafin karewar wa’adin gwamnati mai ci a shekarar 2023.Mele Kyari ya dauki alkawarin ne, bayan karbar jagorancin kamfanin na NNPC daga Dakta Maikanti Baru.

Kyari ya kara da alwashin farfado kara yawan litar man da matatun kasar za su rika tacewa zuwa lita miliyan 3 a kowace rana.

Gwamnatocin Najeriya da suka gabata, sun narka makudan kudade kan kokarin farfado da matatun man kasarda suka durkushe amma hakan bata samu ba.

Zalika gwamnatin shugaban kasar Muhammadu Buhari mai ci a zangon farko ta yi kokarin gyara matatun man, amma suka gaza kaiwa matakin da ake bukata.

A halin yanzu matatun man Najeriyar da ke Warri, Fatakwal, da kuma Kaduna, na iya tace litar danyen mai dubu 445 ne kawai, a wasu lokutan ma adadin ya kan gaza, saboda matsalolin lalacewar wasu kayayyaki.
RFIHausa.

No comments:

Post a Comment