Tuesday, 6 August 2019

A karshe dai an samu wanda ya wuce Van Dijk da kwallo

Wasanni 65 tauraron dan kwallon Liverpool, Virgil Van Dijk ya buga ba tare da an samu dan wasan da ya wuceshi da kwallo ba a matsayin dan baya ba. Saidai wannan bajin ta da yake jan zare a kanta tazo karshe a wasan da suka buga da Manchester City na neman cin kofin Community Shield.Van Dijk ya buga gaba dayan kakar wasan Premier League da Champions League na 2018/19 ba tare da an samu wanda ya wuceshi da kwallo ba amma a wasan da Manchester City ta doke su a bugun daga kai sai mai tsaron gida tare da daukar kofin na Community Shield a ranar Lahadin data gabata, Gabriel Jesus ya wuce Van Dijk da kwallo.

Dan kwallo na karshe da ya wuce Van Dijk da kwallo kamin Jesus shine dan wasan NewCastle, Mikel Merino a watan Maris na shekarar 2018.
 
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment