Saturday, 17 August 2019

Abinda wannan budurwar ta wa saurayin da yace yana sonta ya dauki hankula sosai


Wata matashiya ta sha yabo bisa yanda ta amsa wani saurayi da ya nuna yana sonta a shafin Twitter, ba kamar yanda wasu karara a bainar jama'a ke bayyana basa son mutum ba ko kumama su yi banza ba tare da sun amsa tayin da wasu samari ke musu ba.

Ita dai wannan baiwar Allah ta amsashi duk cewa ya bayyana mata shi talakane bashi da karfi amma yana neman na kansa.

Wannan abu da ta yi yaja mata yabo sosai inda wasu suka rika kiran ga sauran mata musamman a shafin Twitter da su yi koyi da ita.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment